Bitcoin Kamar Wasanni ne
daga @thebitcoinrabbi 2021/01/13open in new window
Yawancin lokaci ina yin bayanin yadda #bitcoin ke aiki kuma an raba shi cikin mahallin wasan wasanni. Na ga cewa yana taimakawa da yawa wajen amsa yawancin tambayoyi gama gari:
Q: Wanene ya ฦirฦira wasan ฦwallon baseball?
A: Gaskiya ba abun damuwa bane. Kowa a duniya yana iya wasa. Ba komai idan ainihin wanda ya ฦirฦira yana son canja ฦaโidojin ko sakawa kansa maki ko wani abu. Ba mu damu da abun da yake tunani game da wasanmu ba.
Q: Wanene yake kula da wasan?
A: Babu wanda yake kula, duka mun yanke shawarar yin wasa ne kawai. Dukanmu mun sani kuma muna aiwatar da dokoki, kuma idan wani ya yi maguษi, zaโa kore shi daga wasan. Idan wani ya bawa kansa ladan maki da bai samu ba, sai mu yi watsi da su.
Q: Ta yaya muka san dokokin ba za su canja ba?
A: Duka mun amince da su lokacin da muka fara wasa, kuma duk wanda ke son ya ci gaba da wasa da waษannan dokokin zai ci gaba, kuma idan wani yana son ya canja su, sai dai ya buga a wani wuri.
Q: Ba zaโa iya kutse ba?
A: Komai a bayyane yake. Dukanmu muna iya ganin dukkan filin da dukkan maki. Idan wani yana magudi, mu duka mun sani kuma mu zamu gaya musu su ษace.
Q: Me yasa ya cancanci wani abu?
A: Dukanmu mun yanke shawarar yin wasa, don haka yana da wata daraja a garemu. Idan wani yana son shiga, dole ne su yarda su amince da dalilanmu da ฦimarmu.
Ina daraja shi, don haka yana da daraja. ฦimar abu ne na zahiri.
Q: Ba zaโa hana shi ba?
A: Watakila, amma wasu ne kawai suke wasa da sanda da kwallo, ba su cutar da kowa ba, don haka gwamnati za ta iya hana ku bugawa, amma ba za su iya hana manufar buga sanda da kwallo ba, wasan zai ci gaba a wani wuri.
Q: Shin zan iya shiga?
A: Yi duk abun da kuke so. Ina jin daษin yin wasan ฦwallon baseball, kuna iya shiga ko kuna iya HFSP.